Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane 12 a Gana

Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane 12 a Gana

Mutane 12 sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruywan da mamakon ruwan sama ya janyo a arewa maso-gabashin Gana.

Jami'in Hukumar Yaki da Annoba ta Arewacin Gana John Kwaku Alhassan ya shaida cewa, sakamakon ruwan saman da ake ci gaba da samu a 'yan kwanakin nan a Nalerigu ambaliya ta afku.

Alhassan ya kara da cewa, mutane 12 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwaan, wasu da dama kuma sun jikkata.

Mutane dubu 1,800 sun rasa matsugunansu inda kasar noma kadada dubu 2 ta lalace.

 

News Source:  TRT (trt.net.tr)