An ciro jikkunan mutane 20 daga cikin wata rijiya a Mekziko

An ciro jikkunan mutane 20 daga  cikin wata rijiya a Mekziko

Sakamakon korafin da aka gabatar, an ciro jikkunan mutane 20 daga cikin wata rijiya a kasar Mekziko.

Labaran da jaridun Mekziko suka fitar sun rawaito mahukuntan jihar Veracruz na cewa, an ciro jikkunan mutanen 20 daga wata rijiya a ke garin Omealca.

Mahukuntan sun ce, masu gabatar da kara ne suka rakiya zuwa rijiyar mai zurfin mit 30 inda bayan bincike aka ciro gawarwakin mutane 20.

An fara aiyukan gano musabbabin mutuwar mutanen.

 

News Source:   ()