An kashe mutane 15 sakamakon harin bam a Afganistan

An kashe mutane 15 sakamakon harin bam a Afganistan

Mutane 15 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kai a lokacin taron jana'izar Shay Akram, kwamandan masu tsaron gundumar Hiva ta lardin Nangarhar din Afganistan.

Kakakin Fadar gwamnan Nagrahra Ataullah Hogani ya fadi cewar an jikkata karin mutane 65 a harin.

Ya ce daga cikin wadanda suka mutu har da Mukaddashin Shugaban Majalisar Shura ta Nangarhar Lala Han, kuma wasu daga cikin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali.

Babu wanda ya dauki alhakin ka harin.

News Source:  www.trt.net.tr