'Yan sanda sun kwashi artabu da masu zanga-zangar Covid-19 a Jamus

'Yan sanda sun kwashi artabu da masu zanga-zangar Covid-19 a Jamus

Jami'an 'yan sanda sun takawa wadanada suka fara gudanar da zanga-zangar kalubalantar sabbin matakai akan yakar kwayar cutar coronavirus.

Wasu kungiya akan titin Linien dake kusa da filin shakatawar Rosa-Luxemburg sun nemi gudanar da tarzoma domin nuna rashin amincewa ga wasu matakan da aka sanya domin dakile yaduwar covid-19.

Jami'an tsaro dai sun rufe filin shakatawar da dukkanin titunan dake kusa dashi.

'Yan sun dinga sanar da cewa an haramta gudanar da zanga-zangar kalubalantar matakan yakar corona inda kuma suka nemi al'umman kowa ya kuma ankinsa.

Wadanda suka ki jin jan kunnen 'yan sanda an cika hannu dasu lamarin da ya sanya kame da yawa daga cikinsu.

 

News Source:  www.trt.net.tr