'Yan ta'addar Daesh sun kai hare-hare a Iraki

'Yan ta'addar Daesh sun kai hare-hare a Iraki

Sakamakon harin da 'yan ta'addar Daesh suka kai a jihar Diyala da ke gabashin Iraki, 'yan tawayen Hashdi Sha'abi 2 da jami'in sojin Iraki 1 sun rasa rayukansu.

Wani jami'in Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Iraki da ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewar, a arewacin jihar Diyala 'yan ta'addar daesh sun kai kan shingen binciken ababan hawa na Hashdi Sha'abi da ke yankin Hawi Al-Azim inda suka kashe kashe 'yan tawaye 2 tare da jikkata wasu 3.

A yankin Ayn Laila na jihar kuma an kashe sojan Iraki 1 bayan harin bindiga da 'yan ta'addar Daesh suka kai.

News Source:  www.trt.net.tr