Bayanin Cavusoglu game da taron Amurka da Jamus kan Afganistan

Bayanin Cavusoglu game da taron Amurka da Jamus kan Afganistan

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya fitar da sanarwa game da taron da ya halarta kan hali da yanayin rikici da ake ciki a Afganistan wanda Amurka da Jamus suka shirya.

A sanarwar da Cavusoglu ya fitar ta shafinsa na Twitter ya shaida cewa, ya halarci taron da Amurka da Jamus suka shirya ta hanyar sadarwar bidiyo inda ya bayyana ra'ayinsa game da halin rikici da jin kai da aka shiga a Afganistan.

A ranar 15 ga Agusta ne Taliban ta kewaye birnin Kabul inda bayan Shugaban Kasar Afganistan Ashraf Gani ya fice daga kasar suka karbe iko da Babban Birnin ba tare da zubar da jini ba.

Kwanaki 2 da suka gabata Taliban ta sanar da kafa gwamnati a Afganistan.

News Source:   ()