Gobara ta kama a birinin Tetovo na Arewacin Macedonia

Gobara ta kama a birinin Tetovo na Arewacin Macedonia

Dangane da bayanan farko, mutane 10 ne suka rasa rayukansu a gobarar da ta kama a tsakiyar birnin Tetovo, inda ake kula da marasa lafiya masu sabon nau'in cutar corona (Covid-19), a yankin arewa maso yamma na Arewacin Macedonia.

Ma'aikatar Lafiya ta Arewacin Macedonia ta sanar da cewa gobara ta kama cikin dare a Tetovo.

A cikin sanarwar Ma'aikatar ta bayyana cewa,

"An tabbatar da cewa mutane 10 sun mutu a gobarar ya zuwa yanzu. Amma adadin zai iya karuwa."

Da ake jaddada cewa an shawo kan gobarar, an lura cewa an mika wadanda suka jikkata zuwa Skopje, babban birnin kasar.

Firaministan Arewacin Macedonia, Zoran Zaev ya bayyana cewa babban bala'i ya afku a sanarwar da ya yada a shafukansa na sada zumunta inda ya ce,

"Gobara ta kama ne sakamakon wata fashewa. An shawo kan gobarar, amma an rasa rayuka da dama. Har yanzu wasu na ci gaba da gwagwarmayar rayuwa." 

Zaev ya jajantawa 'yan uwan wadanda suka rasa rayukansu tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.

News Source:   ()