Gobara ta yi ajalin mutane da dama a gidan kurkukun Indonesia

Gobara ta yi ajalin mutane da dama a gidan kurkukun Indonesia

Fursunoni 41 ne suka rasa rayukansu sakamakon gobarar da ta kama a gidan kurkukun Tangerang da ke kusa da Jakarta Babban Birnin kasar.

Kakakin Ma'aikatar Shari'a da Kare Hakkokin Dan Adam ta Indonesia Rika Apriant ya shaida cewa, gobarar ta faro da ginin mai lambar C da aka kulle wadanda aka tuhuma da safarar miyagun kwayoyi inda fursunoni 41 suka mutu, wasu 39 kuma suka samu raunuka.

An aike da sojoji da 'yan sanda zuwa gidan kurkukun don kashe gobarar da ta kama da karfe dya na dare.

Ba a san musabbabin kamawar gobarar ba.

Fursunoni na ywan yi tawaye da bore a gidajen kurkukun Indonesia da ake ajje su a cunkushe.

 

News Source:   ()