Harin bam ya hallaka mutum 3 a Afghanistan

Harin bam ya hallaka mutum 3 a Afghanistan

A wani hari da aka kai kusa da kofar wani gidan yari da babur dankare da bama-bamai a jihar Lagman dake kasar Afghanistan mutum uku sun rasa rayukansu.

Mai magana da yawun walin Lagman Esadullah Devletzey, ya sanar da cewa an ajiye babur dauke da bama-bamai a kofar shigar wani gidan yari dake tsakiyar Lagman kuma bam din ya fashe.

Devletzey, ya kara da cewa mutum 3 sun rigamu gidan gaskiya inda kuma wasu ma'aikatan gidan wakafin hudu suka raunana.

Kawo yanzu dai ba'a dora alhakin harin akan kowa ba.

 

News Source:  www.trt.net.tr