Marasa lafiya 16 sun mutu a asibiti sakamakon ambaliyar ruwa a Mekziko

Marasa lafiya 16 sun mutu a asibiti sakamakon ambaliyar ruwa a Mekziko

Marasa lafiya 16 da ke wani asibiti sun mutu a ambaliyar ruwan da ta afku sakamakon mamakon ruwan sama a Mekziko.

Dangane da labaran jaridun Mekziko, Asibitin Tsaro na jihar Hidalgo ya cika da ruwa saboda mamakon ruwan sama.

Hukumomi sun sanar da cewa asibitin ya cika da ruwa a cikin mintuna kadan sakamakon kwararar kogin Tula, kuma kayan aikin iskar oxygen sun lalace sakamakon katsewar wutar lantarki.

A cikin bidiyon da aka yada a shafukan sada zumunta, an ga cewa asibitin yana karkashin ruwa kuma ma'aikatan kiwon lafiya sun yi kokarin motsa gadajen marasa lafiyan a cikin ruwan.

Marasa lafiya 16 sun mutu a lamarin.

An bayyana cewa akalla mutane dubu 39,000 ne ambaliyar ruwan ta shafa a fadin jihar.

News Source:   ()