Sojojin gwamnatin Siriya sun kashe fararen hula 4 a Idlib

Sojojin gwamnatin Siriya sun kashe fararen hula 4 a Idlib

Sojojin gwamnatin Siriya sun kai hari yankin Idlib na arewacin kasar tare da kashe fararen hula 4 da jikkata wasu 4.

Dakarun na gwamnati da aka jibge a gundumar Serakib ta kudancin lardin Idlib sun hada da 'yan ta'addar da Iran ke marawa baya. Dakarun sun kai hari ta kasa zuwa ga tsakiyar garin Idlib.

Kungiyar Kare Fararen Hula ta bayyana cewa, fararen hula 4 sun mutu, wasu 2 kuma sun samu raunuka sakamakon harin.

An kai wadanda suka jikkata zuwa asibitocin yankin.

 

News Source:   ()