Sojojin Indiya 2 sun rasa rayukansu a rikici tsakaninsu da na Pakistan

Sojojin Indiya 2 sun rasa rayukansu a rikici tsakaninsu da na Pakistan

An sanar da cewa mayar da martanin da sojojin Pakistan suka yi a lokacin da sojojin Indiya suka kai musu hari a yankin Kashmir ya yi sanadiyar rayukan sojojin Indiya biyu.

Dangane ga bayanan da suka fito daga rundunar sojin Indiya hari ta sama da sojin Pakistan suka kai a sansanin sojojin Uri da ya raba Kashmir biyu ya yi sanadiyar mutuwar sojojinta biyu.

Sanarwar ta kara da cewa wannan harin ya sabawa yarjejeniyar tsagaita wuta ta shekarar 2003.

Haka kuma harin da sojan Indiya suka kai a yankin ya yi sanadiyar mutuwar farar hula daya da kuma jikkata daya.

A dayan barayin kuma a rikicin da ya barke tsakanin ‘yan tada kayan baya da sojojin Indiya a yankin Jammu Kashmir na Indiya ‘yan tawayen biyu sun rasa rayukansu.

News Source:  www.trt.net.tr