Isra'ila ta rage girman yankunan teku da Falasdinawa za su iya kamun kifi

Isra'ila ta rage girman yankunan teku da Falasdinawa za su iya kamun kifi

Isra'ila ta rage tsayi da girman yankunan tekun gabar Zirin Gaza da Falasdinawa za su iya kamun kifi daga mil 12 zuwa mil 6.

Rubutacciyar sanarwar da Ofishin Kula da Aiyukan Gwamnati a Yankunan Falasdinawa ta ce, bayan sake nazari da aka yi kan halin da ake ciki, an rage nisan wajen da za a iya kamun kifi a Zirin Gaza daga mil 12 zuwa mil 6.

Sanarwar ta ce, wannan mataki ya fara aiki nan take kuma har sai zuwa lokacin da aka fitar da wata sanarwar ta daban.

Sanarwar ta kara da cewa, an dauki wannan mataki ne saboda harasan wuta da ake harbawa Isra'İla daga Zirin Gaza.

A ranar 12 ga Yuli ne Isra'ila ta kara nisan yankin da masuntan Zirin Gaza za su iya kamun kifi daga mil 9 zuwa 12.

News Source:   ()