Ambaliyar ruwa ta raba dubunnan daruruwan Somaliyawa da matsugunansu

Ambaliyar ruwa ta raba dubunnan daruruwan Somaliyawa da matsugunansu

Sama da mutane dubu 341 ne suka rasa matsugunansu a watanni 4da suka gabata sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku a Somaliya.

Ofishin Aiyukan Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ya bayyana cewar dubunnan daruruwan mutane sun rsa matsugunansu sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu a kasar.

Mutane dubu dubu 341,884 ne suka bar matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwan da aka samu a Somaliya a watanni 4 da suka gabata.

Yankunan noma da ke kusa da gabar kogin Shabelle ne ambaliyar ruwan ta fi illatawa.

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane miliyan 2,1 na fuskantar hatsarin yunwa.

News Source:  TRT (trt.net.tr)