Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane 131 a Najeriya

Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane 131 a Najeriya

Mutane 131 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan da mamakon ruwan sama ya janyo a Najeriya.

Daraktan Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar Sokoto Mustapha Umar ya shaida cewar, karin mutane 36 sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar da aka samu a jihar.

Daga watan da ya gabata zuwa yau mutane 131 ne suka mutu a Najeriya sakamakon ambaliyar ruwan da aka samu.

Umar ya bayyana cewar ambaliyar ruwan ta raba mutane 470 daga matsugunansu, ta lalata kasar noma hekta dubu 302 da 500 inda shanu 120 suka mutu.

Ya ce, gwamnatin jihar da SEMA na aiyukan bayar da agaji ga wadanda ambaliyar ruwan ta shafa.

 

News Source:  TRT (trt.net.tr)