Ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar hasarar rayuka da dukiya a Najeriya

Ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar hasarar rayuka da dukiya a Najeriya

An sanar da cewa sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ta haifar da ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar hasara rayuka 185 a fadin Najeriya. 

Sakataren Hukumar bayar da agajin gaggawa a ta (NEMA) ta reshen jihar Kano Salih Jili ya bayyana cewa ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar rayukan mutum 54 a fadin jihar.

Jili dake bayyana cewa ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar raba mutum dubu 30 da 356 daga matsuguninsu ya kara da cewa ta kuma lalata gonakin da girmansu ya kai hekta dubu 9 da 127.

Haka kuma ya kara da cewa tuni dai an fara kaiwa alumman da annobar ta shafa dauki. 

Tun farkon watan Agusta kawo yanzu ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar rayuka 185 a fadin Najeriya. 

Ambaliyar da ta shafi ķasashen Najeriya, Nijer, Burkina Faso da Senagal ta haifar hasarar rayuka da dukiya masu yawa.

 

 

News Source:  TRT (trt.net.tr)