An dage zaman shari'ar tsohon Shugaban Sudan Al-Bashir

An dage zaman shari'ar tsohon Shugaban Sudan Al-Bashir

A Sudan an dage zaman Shari'ar tsohon Shugaban Kasar Umar Al-Bashir da aka kifar da gwamnatinsa a ranar 11 ga Afrilun 2019 bayan zanga-zangar da aka fara a 2018.

An dage zaman shari'ar zuwa ranar 15 ga Yuni.

A zaman da aka yi akotu ta musamman a Khartoum Babban Birnin Sudan, mai shari'a Ali Ahmad Ali ya saurari bayanan lauyoyin Al-Bashir.

Lauyoyin Al-Bashir sun bukaci da a hukunta lauyan bangaren gwamnatin soji Abdulkadir Al-Badawi saboda zargin tauye hakkokin alkali Ali a yayin zaman shari'a na ranar 25 ga Mayu.

An dage zaman shari'ar zuwa ranar 15 ga watan Yuni.

A ranar 19 ga Disamban 2018 aka fara zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Sudan, daga baya ta koma adawa da gwamnati, inda a ranar 11 ga Afrilun 2019 sojoji suka kifar da gwamnatin kasar.

News Source:  TRT (trt.net.tr)