An kashe mutane 22 a Najeriya

Mutane 22 sun rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

Labaran da jaridun kasar suka fitar na cewa wasu 'yan bindiga ne suka kai hari a wasu kauyukan yankin Zangon Kataf da ke jihar ta Kaduna inda suka bude wuta kan jama'a.

An kashe mutane 22 tare da jikkata wasu da dama a harin.

Kakakin 'yan sandan jihar Kaduna Muhammad Jalige ya tabbatar da an kai harin, kuma ya ce an yi garkuwa da mutane da dama.

Jalige ya kara da cewar an aike da jami'an tsaro zuwa yankin, kuma an saka dokar hana fita ta awanni 24.

News Source:  www.trt.net.tr