An kashe mutane 3 sakamakon harin bam a Somaliya

An kashe mutane 3 sakamakon harin bam a Somaliya

Mutane 3 sun rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kai da yammacin Litinin din nan a Somaliya.

Kamfanin dillancin labarai na Somaliya ya shaida cewa, a harin ba din da aka kai a gundumar Balcad da ke yankin Lower Shabel, an kashe fararen hula 2 da soja 1, wasu mutane 8 da suka hada da sojoji 6 sun jikkata.

Gwamnati ba ta fitar da wata sanarwa game da harin ba, babu kuma wanda ya dauk alhakin kai harin.

Kungiyar ta'adda ta Al-Shabab na yawan kai hare-hare kan fararen hula da jami'an tsaro a Somaliya.

News Source:  TRT (trt.net.tr)