An kashe mutane 7 a Somaliya

An kashe mutane 7 a Somaliya

Mutane 7 da suka hada da sojoji 2 sun rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai a gundumar Hodan da ke Mogadishu Babban Birnin Somaliya.

An kai harin bam din kan jerin gwanon motocin kwamanda Mahad Abdurrahman.

Kwamandan ya tsira da rayuwarsa, amma an kashe mutane 7 da suka hada da sojoji 2.

 

News Source:  TRT (trt.net.tr)