An kashe sojoji 6 a hare-haren ta'addanci a Mali

An kashe sojoji 6 a hare-haren ta'addanci a Mali

Sojoji 6 sun rasa rayukansu sakamakon hare-haren ta'addanci 2 da aka kai a yankuna daban-daban na Mali.

An kai hare-haren ta'addanci a lokaci guda kan sansanonin sojin Mali da ke garuruwan Boulkessi da Mondoro.

Sojojin Mali 6 sun mutu, an kuma kassara 'yan ta'adda 40 a fafatawar da aka yi.

News Source:  TRT (trt.net.tr)