An sace mutum 40 a jihar Zamfara dake Najeriya

An sace mutum 40 a jihar Zamfara dake Najeriya

Wasu 'yan bindiga da ake zatun masu kame mutane ne domin karbar kudin fansa sun kai hari a wani Masallaci dake jihar Zamfara dake Najeriya inda suka kashe mutum 5 da kuma yin awon gaba da 40.

Maharan da ba'a san ko su wanene ba sun bayyana a Masallacin ne saman babura.

Tuni dai jami'an tsaro sun kewaye yankin inda suka fara bincike akan lamarin.

A jihar Zamfara dai an dauki kusan shekaru hudu ana dauki ba dadi tsakanin manoma da makiyaya.

A yayinda makiyaya ke zargin ana sace musu dabbobi, manoma na zargin makiyaya na lalata musu amfanin gona.

A yankin dai an bayyana cewa an kashe kusan mutum dubu biyu inda dubbai kuma suka rasa mastugunansu sakamakon rikicin.

 

News Source:  TRT (trt.net.tr)