An saka dokar hana fita waje a Jamhoriyar Afirka ta Tsakiya

An saka dokar hana fita waje a Jamhoriyar Afirka ta Tsakiya

An saka dokar hana fita waje a Jamhoriyar Afirka ta Tsakiya domin daukar matakan kara tabbatar da tsaro a kasar.

Mai magana da yawun ministan sadarwar kasar Albert Yaloke Mokpem ne ya bayyana a kafar radiyon kasar da cewa shugaban kasar Jamhoriyar Afirka ta Tsakiya ya bayyana saka dokar hana fita waje tsakanin karfe 20.00-05.00. 

Matakan na Yaloke Mokpem ya kasance ne domin kauda hare-hare a kasar.

A shekaran jiye ne dai hadakar kungiyar CPC dake kasar sun ka kai hari a yankunan garuruwan Buar da Grimari dake kudu maso yammacin kasar.

 

News Source:  TRT (trt.net.tr)