An sake zartar da hukuncin kisa kan fursunoni 13 a Masar

An sake zartar da hukuncin kisa kan fursunoni 13 a Masar

Shafin Facebbok na tashar talabijin ta Vatan mai yada shirye-shirye a kasashen waje da ke da alaka da Kungiyar 'Yan uwa Musulmi ta Masar ya bayyana cewar, an sake zartar da hukuncin kisa kan wasu fursunoni 13.

Shafin ya fitar da jerin sunayen mutanen 13.

Haka zalika tashohin talabijin na Mukemmelin da Shark da ke wajen Masar ma sun bayar da labarin zartar da hukuncin kisan kan fursunonin siyasa 13.

Tashar Shark ta bayar da bayanai game da kashe mutanen 13, kuma an bukaci makusantansu da su je asibitin Zinhum da ke Alkahira don daukar gawarwakinsu.

Babu wata sanarwa da mahukuntan Masar suka fitar game da lamarin.

Tun bayan juyin mulkin soji a Masar a 2013 mutane da dama sun fuskanci hukuncin kisa a kasar inda ke kuma zartar musu da shi.

News Source:  TRT (trt.net.tr)