An soke hukuncin daure wasu 'yan majalisar dokokin Tunisiya

An soke hukuncin daure wasu 'yan majalisar dokokin Tunisiya

A Tunisiya an soke hukuncin da aka dauka na kamawa tare da daure wasu 'yan majalisar dokoki 4 da wani lauya 1.

Alkalin kotun soji a Tunus Babban Birnin Kasar ya yanke hukuncin soke matakin kama 'yan majalisar dokoki da suka hada da Shugaban Jam'iyyar Kawance Sayfaddin Mahluf, Abdullatif al-Alawi, Muhammad Abbas, Mahir Zayd da kuma lauya Mahdi Zagruba.

Kotun ta yanke wannan hukunci bisa dogaro da cewa, sai an gama bin wasu hanyoyi na doka sannan za a iya aiwatar da matakin kama su.

A watan Maris ne a filin tashi da saukar jiragen saman Tunus jami'an tsaro suka hana wata mace fita daga kasar ba tare da zargin ta da aikata wani laifi ba.

A wannan lokaci Shugaban Jam'iyyar Kawance Sayfaddin Mahluf, Abdullatif al-Alawi, Muhammad Abbas, Mahir Zayd da kuma lauya Mahdi Zagruba na a filin jirgin inda suka kuma kare matar.

Daga baya an gano a lokacin da hakan ta faru, ana aik, da dokar hana wadanda ake zargi da aikata ta'addanci fita kasar waje. Doka ce daka asamar a zamanin hambararren Shugaban Tunisiya Zeynel Abidin bin Ali.

A ranar 31 ga watan Yuli kotun soji ta Tunisiya ta bayar da umarnin kama 'yan majalisar dokoki na jam'iyyar Kawance su 4.

News Source:  TRT (trt.net.tr)