'Yan bindiga sun kashe mutane 12 a Najeriya

'Yan bindiga sun kashe mutane 12 a Najeriya

Mutane 12 sun rasa rayukansu sakamakon harin 'Yan bindiga a wasu kauyukan Najeriya.

Labaran da jaridun kasar suka fitar sun bayyana cewa, wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai hari a kauyukan yankin Kauru na jihar Kaduna.

Mutane 12 da suka hada da dan sanda 1 sun mutu, wasu da dama kuma sun jikkata sakamakon harin.

Sakamakon yadda ake yawan samun kai hare-hare a kan babura a wasu jihohin kasar, an hana hawa baburan.

 

News Source:  TRT (trt.net.tr)