'Yan ta'addar Al-Shabab 60 sun mutu a wani gida a Somaliya

'Yan ta'addar Al-Shabab 60 sun mutu a wani gida a Somaliya

A kalla 'yan ta'addar Al-Shabab 60 aka bayyana sun mutu sakamakon fashewar wasu abubuwa a wani gida da suke zama a Somaliya.

Wani jami'in soji ya fitar da sanarwa ta gidan rediyon kasa na Somaliya inda ya bayyana cewa, a kalla 'yan ta'addar Al-Shabab 60 ne suka mutu sakamakon fashewar bama-bamai a wani gida da kwararrun hada bam na kungiyar da wasu mambobinta suke ciki a garin Ala-Futow na yankin Lower Shabelle.

Wata mace da yaro karami da ke kusa da gidan mai daki 11 sun rasa rayukansu sakamakon fashewar abubuwan.

Jami'an soji sun sanar da cewa, daya daga cikin 'yan ta'addar kasashen waje 6 da suka mutu a gidan Ahmad Sharif ne da ya je Somaliya daga Afganistan.

Sojojin Somaliya sun bayyana kashe 'yan ta'addar Al-Shabab sama da 100 a makonni 3 da suka gabata karkashin farmakan da suka fara kai musu a yankin Lower Shabelle.

News Source:  TRT (trt.net.tr)