Covid-19: Za a bude makarantu a Zambiya

Covid-19: Za a bude makarantu a Zambiya

Gwamnatin Zambiya ta dauki matakin bude makarantun kasar sakamakon sassauta matakan hana yaduwar annobar Corona da aka yi.

Kakakin gwamnatin Zambiya Amos Malupenga ya ja hankali kan yadda adadin masu kamuwa da Corona a kasar yake raguwa sosai.

Malupenga ya kara da cewa, daga ranar 5 ga Agusta za a fara bayar da karatu a wasu ajujuwan makarantun Zambiya, jami'o'i da sauran manyan makarantu kuma za su ci gaba da koyo da koyarwa ta yanar gizo.

A gefe guda, an bayyana dakunan wasanni za su ci gaba da kasancewa a rufe har tsawon makonni 3.

Sama da mutane dubu 3,400 cutar Corona ta yi ajali a Zambiya daga cikin kusan mutane dubu 197 da ta kama.

News Source:  TRT (trt.net.tr)