Hukunci ga masu amfani da Twitter a Najeriya

Hukunci ga masu amfani da Twitter a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta dauki matakin gurfanar da duk wadanda suka kuskura suka karya dokar da ta saka ta hana amfani da shafin Twitter a kasar.

Kakakin Ma'aikatar Shari'a Umar Jibril Gwandu ya sanar da cewa, Ministan Shari'a kuma Babban Mai Gabatar da Kara da Gwamnatin Tarayya Abubakar Malami ya bayar da umarnin a gurfanar da duk wanda ya karya dokar a gaban kotu.

Malami ya ce, domin gaggauta hukunta wadanda suka karya dokar za a hda kai da Ma'aikatar Yada Labarai da ta Tattalin Arzikin Sadarwar Zamani.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kalaman cewa, za su tunawa tsagerun da ke tayar da zaune tsaye da kona gine-ginen gwamnati da kashe jami'an tsaro a kudu maso-gabashin Najeriya irin yadda ta wakana a lokacin yakin basasar da aka yi a tsakanin 1967-1970, kuma za su yi magana da tsagerun da yaren da suke ji.

Shafin Twitter ya goge wannan kalami na Shugaban Najeriya, wanda hakan ya sanya gwamnatin kasar rufe shafin a kasar a ranar 4 ga Yuni.

News Source:  TRT (trt.net.tr)