Jirgin ruwan bakin haure ya kife a Tunisiya

Jirgin ruwan bakin haure ya kife a Tunisiya

Jirgin ruwan bakin haure ya kife a gabar tekun garin Sfaks na kudancin Tunisiya inda rahotanni suka tabbatar da mutuwar mutane 11.

Wani jami'in tsaro da ke garin Sfaks ya bayyana cewar jirgin ruwan na kasar Tunisiya dauke da bakin haure su 27 ya kife a gabar Mutemediyye Cebenyane.

jami'in ya ce an gano gawarwakin mutane 11, an kubutar da 7 inda ake ci gaba da neman sauran da suka bata.

Jami'in ya kara da cewar 8 daga wadanda suka mutu mata ne, sai kuma yara kanana 3.

Haka zalika ya bayyana cewar dukkan mutanen sun fito ne daga kasashen Afirka.

News Source:  TRT (trt.net.tr)