Jirgin saman soji ya fado a Tunisiya

Jirgin saman soji ya fado a Tunisiya

Wani jirgin saman soji samfurin F-5 ya fado a yankin Tatawin na kasar Tunisiya inda aka bayyana mutuwar matukin sa.

Sanarwar da aka fitar daga Ma'aikatar Tsaron Kasa ta Tunisiya ta bayyana cewar jirgin samfurin F-5 mallakar Rundunar Sojin Saman kasar ya fado a cikin sahara a yankin Tatawin.

An bayyana cewar jirgin ya fado a yayin gudanar da bincike a yankin Remada na Tatawin da ke kudancin Tunisiya, kuma matukinsa ya mutu, inda tuni aka kafa kwamitin da zai binciki lamarin.

Sanarwar ba ta bayar da bayanai game da musabbabin fadowar jirgin ba.

News Source:  TRT (trt.net.tr)