Kungiyar ta'adda ta Al-Shabab ta kashe sojoji 13 a Somaliya

Kungiyar ta'adda ta Al-Shabab ta kashe sojoji 13 a Somaliya

Sojoji 13 sun rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan ta'addar Al-Shabab suka kai kan jerin gwanon motocin sojoji a Somaliya.

Labaran da jaridun kasar suka sun rawaito Manjo Muhammad Ali na cewa, 'yan ta'addar Al-Shabab sun kai musu hari a yankin Afgoye mai nisan kilomita 30 kusu maso-yamma da Mogadishu babban birnin kasar.

Ya ce, arangama ta barke bayan kai harin idan aka kashe 'yan ta'addar Al-Shabab da dama.

Ali ya kuma ce a kalla sojoji 13 ne suka mutu sakamakon harin.

Ya kara da cewar dakarun Somaliya na sintiri a yankin.

News Source:  TRT (trt.net.tr)