Libiya: Muna tare da hukunce-hukuncen da aka yanke a Babban Taron Berlin

Libiya: Muna tare da hukunce-hukuncen da aka yanke a Babban Taron Berlin

Majalisar Gudanarwar Libiya ta bayyana cewar tana tare da hukunce-hukuncen da aka yanke a Babban Taron Berlin.

Bayan taron da Majalisar ta gudanar a Tarabulus Babban Birnin Libiya, ta fitar da rubutacciyar sanarwa inda aka yi bayani da karin haske kan yanayin siyasar Libiya, tsaro, sojoji da kuma irin manufofin kasashen waje a cikin kasar.

Sanarwar ta kuma jaddada cewar Libiya na tare da hukunce-hukuncen da aka yanke a Babban Taron Berlin.

A taron da aka gudanar a ranar 19 ga Janairun bana wanda bangarorin da ke rikici da juna suka halarta a Berlin Babban Birinin Jamus, an yi kira da a tsagaita wuta.

News Source:  TRT (trt.net.tr)