Morokko za ta fara bayar da shaidar yin allurar riga-kafin Corona

Morokko za ta fara bayar da shaidar yin allurar riga-kafin Corona

Gwamnatin Morokko ta bayyana cewa, za ta fara bayar da fasfo da ke nuna shaidar an yiwa mutum allurar riga-kafin cutar Corona sau 2.

Rubutacciyar sanarwar da gwamnatin Morokko ta fitar ta bayyana cewa, sakamakon bukatar da kwamitin kwararru kan yaki da Corona ya gabatar, za a bayar da fasfon shaidar karbar allurar riga-kafin Corona sau biyu domin kara karfafa aiyukan yaki da annobar.

Wadanda aka baiwa fasfon riga-kafin za su iya yawo a cikin kasar ba tare da wata tsangwama ba, sannan za su iya fita da shiga Morokko cikin sauki.

News Source:  TRT (trt.net.tr)