Mummunan hatsarin jirgin ruwa a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

Mummunan hatsarin jirgin ruwa a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

Mutane 25 sun rasa rayukansu sakamakon hatsarin jirgin ruwa a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Mataimakin gwamnan jihar Tshopo Maurice Abibu Sakapela ya shaida cewa, wani jirgin ruwa da ya tashi daga Kisangani zuwa Basoko ya kife sakamakon loda masa kayan da suka wuce kima.

An bayyana mutuwar mutane 25 tare da bacewar wasu 19 sakamakon hatsarin.

Ana ci gaba da neman wadanda suka bata.

 

News Source:  TRT (trt.net.tr)