Sojojin Somaliya sun kwace wasu yankunan kasar daga hannun Al-Shabab

Sojojin Somaliya sun kwace wasu yankunan kasar daga hannun Al-Shabab

Sakamakon farmakan da ta kai a jihar Galgumud, rundunar sojin Somaliya ta kwace garuruwa 4 da kauyuka 8 daga hannun 'yan ta'addar Al-Shabab.

Tashar talabijin ta kasa ta Somaliya (SNTV) ta shaida cewa, kusan makonni 3 da suka gabata aka fara kai farmakai a yankin Mudog inda aka kashe 'yan ta'addar Al-Shabab sama da 200.

A yayin farmakan an rushe sansanonin Al-Shabab 16, an kuma kwace garuruwa 4 da kauyuka 8 daga hannun 'yan ta'addar.

A 'yan watannin nan sojojin Somaliya sun tsaurara kai farmakai kan 'yan ta'addar Al-Shabab a yankunan kasar daban-daban.

 

News Source:  TRT (trt.net.tr)