Tsohon Shugaban Kasar Nijar Mamadou ya rasu

Tsohon Shugaban Kasar Nijar Mamadou ya rasu

Tsohon Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijar Tandja Mamadou ya rasu.

Rubutacciyar sanarwar da gwamnati ta fitar ta ce, Mamadou mai sheksru 82 ya rasu a wani asibiti da ake kula da lafiyarsa a Yamai Babban Birnin Nijar.

An sanar da zaman makoki na kwanaki 3 a Nijar sakamakon rasuwar Mamadou.

A shekarar 1999 Tandja Mamadou ya zama Shugaban Kasar Nijar, an zabe shi a karo na 2 inda ya yi mulki har zuwa 2010.

An kifar da shi daga kan mulki sakamakon juyin mulkin da aka yi a ranar 18 ga Fabrairun 2010.

 

News Source:  TRT (trt.net.tr)