Uganda ta takaita amfani da shafukan sada zumunta kwanaki 2 kafin zabe

Uganda ta takaita amfani da shafukan sada zumunta kwanaki 2 kafin zabe

Gwamnatin Uganda ta takaita dukkan shafukan sada zumunta gabanin babban zaben ranar 14 ga Janairu.

Jaridar The Daily Monitor ta rawaito cewa Hukumar Sadarwa ta Uganda (UCC) ta umarci masu ba da sabis na yanar gizo da su takaita dukkan shafukan sada zumunta da manhajojin aika sakonni.

A cikin wannan umarnin, Babban Darakta na UCC Irene Sewankambo cikin gaggawa ta nemi kamfanonin sadarwa da su dakatar da damar amfani da shafukan sada zumunta da manhajojin aika sakonni.

Kakakin fadar shugaban kasar Uganda, Don Wanyama ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana cewar sun rufe asusuna Facebook da ke goyon bayan shugaban kasar na yanzu, Yoweri Museveni.

Facebook ya yanke shawarar rufe wasu asusuna da ke goyon bayan Museveni, da cewa "ba asusunan mutanen gaske ba ne”.

Ana ganin Mawaki Robert Kyagulanyi, wanda aka fi sani da "Bobi Wine" a matsayin babban abokin hamayyar Shugaba Museveni, wanda ke kan karagar mulki tun daga zaben 14 ga Janairun 1986.

News Source:  TRT (trt.net.tr)