Zabe a Gini: Shugaba Conde na kan gaba

Zabe a Gini: Shugaba Conde na kan gaba

Sakamakon Zaben Shugaban Kasar Gini na cewa, Shugaba Alpha Conde na kan gaba a yankuna 4 na kasar.

An samu sakamakon farko na zaben da aka aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata. Shugaba mai ci Alpha Conde ya samu nasara a yankuna 4.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta sanar da sakamakon da aka samu na zaben da aka yi a ranar 18 ga Oktoba a yankunan Kaloum, Boffa, Matoto da Matam.

Sakamakon ya nuna cewar Shugaba Conde ya samu kaso 49 a Matoto, 51 a Kaloum, 56 a Boffa da 51 a Matam cikin dari na kuri'un da aka jefa.

Babban abokin hamayyar Conde Cellou Dalein Dialloya samu kaso 40 a Matoto, 36 a Kaloum, 29 a Boffa da 37 a Matam.

Hukumar za ta ci gaba da sanar da sakamakon zabukan yankunan.

News Source:  TRT (trt.net.tr)