Game Da Mu

Gaskia TV ita ce tashar talabijin ta tauraron dan adam ta farko daga kasar Ghana wanda ke alaka da masu jin harshen Hausa a duk duniya tare da sakon Musulunci.

An kafa shi ne a babban birnin kasar Ghana, wato Accra, tashar da ta isa mafi yawan sassan Afirka da kuma wasu sassan Turai da Asiya, ta kware kan watsa shirye-shirye, ingantaccen labarai, da sahihan shirye shiryen  addinin Musulunci.

Daga cikin muhimman abubuwan da Gaskia TV ta dau alhakin yadawa jama,a sun hada da ilmantarwa da kuma nishadantar da masu sauraro game da abubuwan da ke faruwa a duniya wanda wakilanta suka tattaro a fadin duniya.

Gaskia TV tana cike da ma'aikata dake aiki tukuru kuma ke magana da harshen Hausa masu cikakken sani da gogewa a aikin watsa labarai da aikin jarida.

Tare da wannan tawaga, Gaskia TV za ta taka muhimmiyar rawa wajen jawo mutanen da ke magana da harshen Hausa wurin yada inganttaccen sakkonnin musulunci tare da kokarin samar da muhimmun tasiri a rayuwan masu kallo.

Gaskia TV kyautar tauraron ku na tauraron dan adam ce, wacce ke ba da shirye-shirye iri-iri. Wasu shirye-shiryen da zaku iya kallo sune labarai, shirye-shiryen tattaunawa, wasanni, kasuwanci, kiwon lafiya, al'amuran zamantakewa na yau da kullum da fina-finai. Ta hanyar kallon Gaskia TV zaka iya koyan karatun Qur'ani daidai, koyan yaren Larabci, majigin yara wato cartoon da shirye-shiryen yara iri daban-daban.

Duk inda kake a duniya, zaka iya Kamo talabijin Gaskia TV kai tsaye domin kuwa muna gabatar da shirye shiryen mu  kai tsaye a kafafen sada zumunta don baka damar koyo da jin daɗi a cikin yanayin natsuwa, kwanciyar hankali da sahihanci.