Abin al'ajabi: Rana uku sun fito a kasar China

Abin al'ajabi: Rana uku sun fito a kasar China

Al'umman jihar Heilongjiang dake arewacin China sun wayi gari da abin ban al'ajabi inda suka ga fitowar rana har guda uku.

A hakikanin gaskiya rana daya ce kawai ta gaskiya sauran biyun kawai alamamomi ne.

Wannan yanayin da aka fi sani da sunan "Parheli" ya ci gaba har na awanni.

Parheli, ko rana ta ƙarya, na samuwa ne ta hanyar hasakakawa daga  ƙananan lu'ulu'u na kankara a sararin samaniya.

 

News Source:   ()