Ambaliyar ruwa a Indonesiya

Ambaliyar ruwa a Indonesiya

Mutane 13 sun mutu, wasu 46 sun bata sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku a jihar Sulawesi ta Kudu da ke Indonesiya.

Jaridar Kompas ta bayyana cewar mamakon ruwan saman da aka samu a yankin Arewacin Luwu ya janyo cikar kogin Masamba.

Mahukunta sun ce ambaliyar ta illata sama da mutane dubu 4, kuma ya zuwa yanzu mutane 13 sun mutu yayinda aka nemi wasu 46 aka rasa.

Ana ci gaba da aiyukan neman wadanda suka bata a yankin.

News Source:  www.trt.net.tr