Amurka ta kashe fararen hula 86 a Yaman

Amurka ta kashe fararen hula 86 a Yaman

An bayyana cewar daga shekarar 2017 zuwa yau Amurka ta kashe fararen hula 86 a hare-haren da ta kai a Yaman.

Cibiyar AirWars da ke Ingila ce ta gudanar da bincike kan hare-haren da Amurka ta kai a yankunan fararen hula a Yaman.

Rahoton AirWars ya bayyana cewar daga shekarar 2017 zuwa yau Amurka ta ka hare-hare sau 190 tare da kashe fararen hula 86.

A bayanin da Hukumar Tsaro ta Amurka ta mikawa majalisar dokokin kasar a shekarun 2018 da 2019 ta ce ba su kashe farar hula ko daya a Yaman ba.

 

News Source:   ()