An gano bakin akwatin jirgin da ya yi hatsari a Indonesiya

An gano bakin akwatin jirgin da ya yi hatsari a Indonesiya

An gano bakin akwatin jirgin kasar Indonesiya da ya yi hatsari a ranar 9 ga watan Janairu a cikin teku.

Hukumar bincike da ceto ta kasar Indonesiya ce ta sanar da cewa an yi nasarar gano bakin akwatin jirgin da ya fada cikin tekkun kuma na kai shi a cibiyar bincike.

Bayan binciken ne dai za'a iya gano dalili faduwar jirgin. Ministan sufuri Budi Karya Sumadi ya sanar da cewa a ranar 9 ga watan jasnairiu ne mintuna biyar bayan tashin jirgin mai lamba "SJ182" dauke da fasinjoji 50 da ma'aikata 12 aka bar jin doriyarsa wanda daga bisani aka gano ya fadi a tsakiyar tsibirin Laki da Lancang dake arewacin Jakarta.

 

News Source:   ()