An gudanar da zanga-zangar kalubalantar Armenia a ltaliya

An gudanar da zanga-zangar kalubalantar Armenia a ltaliya

Ýan ķasar Azerbaijan mazauna ķasar ltaliya sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga Azerbaijan da kuma kalubalantar hare-haren bama bamai da Armenia ke kaiwa a yankin Nagorno Karabakh. 

Kimanin mutum 300 ne suka yi cincirindo a gaban ginar Majalisar kasar dake babban birnin ķasar watau Roma a kusa da filin shakatawar  Montecitorio domin nuna goyon baya ga Azerbaijan da kuma kalubalantar hare-haren bama baman da Armenia ke yiwa yankin Nagorno Karabakh.

Alumman dauke da tutocin Turkiyya dana Azerbaijan sun dinga rera cewa "Karabakh ta Azerbaijan ce", "Kisan kiyashin Khojaly", " A yiwa Khojaly adalci", "A dakatar da harin da Armenia ke kaiwa" da kuma ana kashe farar hula a Ganja. 

 

News Source:   ()