An kai harin kunar bakin wake a Libiya

An sanar da kai wani harin kunan bakin wake a Tripoli babban birnin ķasar Libiya. 

Mai bayar da shawara a ma'aikatar harkokin lifiyar kasar Amin Al Hashim ne ya sanar da cewa harin kunan bakin waken ya afku ne daidai da wani kelenkeluwa  akan titin garin Janzur dake Tripoli babban kasar.

Fadar gwamnatin yankin Jañzur ta sanar da cewa dan kunar bakin waken ya tayar da bam din dake jikkinsa gabanin yan sanda su kama shi.

An bayyyana cewa kasancewar harin ya faru ne da sanyin safiya babu mutane da yawa a inda lamarin ya afku.

Kawo yanzu dai ba'a bayyana wanda ya kai harin da ko mutane nawa suka rasu da jikkata ba.

 

 

News Source:   ()