An kashe 'yan ta'addar Daesh 7 a Iraki

An kashe 'yan ta'addar Daesh 7 a Iraki

A dazukan yankin Kirkuk na kasar Iraki, an kashe 'yan ta'addar Daesh 7 a wasu farmakai da aka kai musu.

An fara kaiwa 'yan ta'addar Daesh farmakai a kusa da gundumar Hawice da ke kudancin Kirkuk.

A farmakan da Kawancen Kasashen Duniya da Amurka ke marawa baya suka bayar da taimako ta sama, an ragargaza mafakar 'yan ta'addar Daesh 7 a kusa da Wadin Shay inda aka kashe mambobin kungiyar 7.

Sojojin Iraki za su ci gaba da aiyuka a yankin har nan da kwanaki 2 masu zuwa.

News Source:   ()