An kashe 'yan tawayen Houthi 'yan Shi'a 23 a Yaman

An kashe 'yan tawayen Houthi 'yan Shi'a 23 a Yaman

Rundunar sojin Yaman ta bayyana kashe 'yan tawayen Houthi 'yan Shi'a da Iran ke goyawa baya sakamakon arangamar da suka gwabza a garin Ma'arib.

Shafin yanar gizo na "September Net" ya fitar da rubutacciyar sanarwar cewa, dakarun sojin Yaman sun gwabza fada da 'yan tawayen Houthi a yankin Al-Kassara na yammacin Ma'arib.

Sanarwar ta kara da cewa, an kashe 'yan tawayen Houthi 23 inda aka kuma lalata motocin sojin Yaman 6.

'Yan tawayen Houthi ba su ce komai ba game da wannan batu.

 

News Source:   ()