An kashe 'yan a ware 8 a Jammu-Kashmir

An kashe 'yan a ware 8 a Jammu-Kashmir

'Yan a ware 8 aka kashe a rikicin da suka fafata da jami'an tsaro a yankin Jammu-Kashmir na Indiya.

jami'an 'yan sanda sun bayyana cewar sun kai wasu farmakai a yankin bayan samun labarin ganin 'yan a waren.

A yayin kai farmakan ne arangama ta balle tsakanin 'yan tawayen da jami'an soji, inda aka kashe 'yan a ware 8.

A 'yan kwanakin da suka gabata ma an kashe 'yan a ware sama da 24 a yankin.

 

News Source:  www.trt.net.tr