An kashe farar hula 1 a yankin Rasul Ayn na Siriya

An kashe farar hula 1 a yankin Rasul Ayn na Siriya

Farar hula 1 ya rasa ransa sakamakon harin bam da aka kai da babur a yankin Rasul Ayn da ke arewacin kasar Siriya.

Wani bam da aka makala a jikin wani babur ne aka tayar daga nesa a yankin Manajir da ke karkashin yankin Rasul Ayn da aka fatattaki 'yan ta'adda daga cikinsa a lokacin kai farmakan Koramar Zaman Lafiya.

Farar hula 1 ya rasa ransa sakamakon harin, wasu gine-gine da ke kusa da wajen sun samu matsala.

Jami'an tsaro sun bayyana cewar akwai yiwuwar 'yan ta'addar aware na YPG/PKK ne suka kai harin.

'Yan ta'addar aware na YPG/PKK da ke ci gaba da mamayar yankunan Ayn Isa da Tel Amir, na yawan kai fare-haren ta'addanci a yankunan Rasul Ayn da Tel Abyad.

News Source:  www.trt.net.tr